Basarake da wani dattijo sun tabbatar da asalin mahaifiyar Atiku a Jigawa

0

Wani dattijo da ya ce ya kusa shekara 100, ya shaida cewa shi kawu ne ga mahaifiyar Atiku Abubakar.

Dattijon mai suna Isyaku Adamu, ya shaida wa manema labarai a jiya Talace cewa a can kauyen da ya ke mai suna Jigawar Sarki, can ne asalin mahaifiyar ta Atiku Abubakar, a Jihar Jigawa.

Jigawar Sarki wani kauye ne a karkashin Karamar Hukumar Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.

Manema labarai sun dira kauyen Jigawar Sarki jiya Laraba, inda suka samu Isyaku Adamu a gidan sa. Ya shaida musu cewa sunan mahaifiyar Atiku Aisha, amma an fi kiran ta Kande Yar-Malam.

Ta auri mahaifin Atiku Abubakar ne bayan da ta rabu da mijin ta na farko.

Ya kara da cewa sunan mahaifin Atiku Garba, kuma malami ne da ya taso daga Sokoto ya zo Jigawar Sarki ya zauna neman imi. A can ne ya ga Kande har aka aura masa ita.

“A wannan gidan na mu ya zauna da ya zo. Ana kiran gidan mu Gidan Malamai. A nan ya ga Kande ya aure ta, daga nan kuma suka yi gaba, ya wuce da ita inda a yanzu ake kira Jihar Adamawa, inda suka haifi Atiku.

“Ita Kande mahaifiyar Atiku ai kanwa ce ga Alhaji Ali da kuma Azumi. Amma duk sun mutu. Kande ‘yar mu ce, Atiku kuma jikan mu ne. Dukkan mu Fulani ne, shi ya sa ake kiran gidan mu Gidan Malamai.”

Wani basarake ne daga cikin masu rike da sarautar gargajiya a Jihar Jigawa ya labarta wa manema labarai inda kauyen ya ke, kuma ya yi musu kwatance.

Sai dai kuma ya nemi su sakaya sunan sa, domin kada a maida abin da ya yi a matsayin siyasa har a kai ga yi masa yarfe.

Basaraken ya ce a can Jigawar Sarki nan ne asalin mahaifiyar Atiku, kuma sunan mahaifin ta Abdullahi.

“Akwai ma wani kawun ta mai suna Abdullahi Adamu, wanda shi ne Babban Limamin Babban Masallacin Dutse, amma ya rasu shekara biyar bayan kirkiro Jihar Jigawa, cikin 1991.”

Share.

game da Author