BARNO: Sojoji sun kwashe mazauna garin da ake zargin Boko Haram na samun mafaka

0

Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta umarci mazauna kauyen Jakana da su gaggauta ficewa daga garin gaba daya.

Hakan ta faru ne bayan yawaitar samun rahotannin cewa Boko Haram na shiga cikin garin su na boyewa ba.

Kauyen Jakana ya na da tazarar kilomita 40 tsakanin sa da Maiduguri, babban birnin Jihar Barno.

Kafin Disamba, 2018 dai Boko Haram ba su taba yin galabar tarwatsa Jakana ba, duk kuwa da hare-haren da suka rika kaiwa. Saboda an ce mutanen garin jajirtattu ne kwarai.

Bayan harin da aka kai Jakana cikin Disamba, Boko Haram sun sake yin galabar shiga garin cikin Janairu da ya gabata, inda har suka banka wa sansanin sojiji da ofishin ‘yan sanda wuta.

Mahukuntan soja sun ce Boko Haram syn samu gindin zama a garin tun bayan harin cikin watan Janairu.

An jima yi zargin cewa wasu mutanen garin na hada baki da Boko Haram wajen ba su mabuya da kuma tsegunta musu bayanai.

Jiya Talata an rika ganin motoci bas-bas cike makil da lodin mutanen Jakana, ta na sauke lodin su a Sansanin Masu Gudun Hijira na Bakasi.

Wani dan ganin da shi ma aka kawo shi aka jibge a Bakasi, mai suna Modu Babagana, ya shaida wa ‘yan jarida cewa: “Ni dai ban taba jin an ce ga wani dan Boko Haram na samun mafaka a Jakana ba. Watakila idan har sojoji sun tabbatar da haka, to sai dai ko.daga bangaren mutanen da ke hijira zuwa garin na m ne, amma dai ba daga mu ba.”

Da yawa da aka yi hira da su cikin wadanda aka kwaso daga Maiduguri, aka jibge sansanin Bakasi a Barno, sun yi kukan cewa an kwaso su babu shiru, ba a bari sun dauko ko da tsinken sakace ba.

Sai dai kuma Kakakin ‘Operation Lafiya Dole’, Ado Musa, ya ce an kwashe mazauna garin zuwan sansanin mash gudun hijira ne domin yin sintirin kakkabe Boko Haram a yankin.

Ya ce da zaran an kammala aikin, to za a gaggauta maida kowa gidan sa.

Amma bai fadi ranar da za a kammala ko kuma ranar da za a maida su din ba.

Hukumar Again Gaggawa ta Jihar Barno ta tabbatar da kwasar mazauna Jakana da ake yi zuwa sansanin masu gudun hijira.

Share.

game da Author