Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya shawarci Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo cewa kada ma ya yi tunanin za a bada fifiko wajen tsaida shi a matsayin wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2023, mai zuwa nan da shekaru hudu.
APC sun rika yin kamfen a zaben 2023 da aka kamnala bayan0gabayan nan cewa idan Buhari ya ci zabe, kuma ya kammala zangon sa na biyu, to yankin Kudu maso Yamma za a bai wa mulki.
Wadannan maganganu sun haifar da sa-in-sa tsakanin ‘yan yankin Kudu maso Yamma, wato Yarabawa da yankin Kudu Maso Gabas, wato kabilar Igbo.
Osita Ikechukwu da Joe Igbokwe, dukkan su manyan APC daga Gabas da Yamma, sun rika ragargazar juna da kuma watsa farfaganda cewa kowa yankin sa ne ya fi cancanta.
Amma shi kuma Babachir Lawal, wanda tsohon makusancin Shugaba Buhari ne, cewa ya yi babu inda APC ta yi alkawarin cewa za a bai wa Osinbajo mulki bayan kammala wa’adin Buhari mulki a 2023.
“Tunda dai wannan magana babu ita a cikin dokar Najriya, don haka ba za a iya rike ta a mtsayin wata yarjejeniya ko alkawarin da za a tilasta cika shi ba.”
Lawal ya ce ba ya na nukura da bayar da mulki ga ‘yan Kudu maso Yamma ba. Amma tunda dai ba doka ko tsarin APC ya yi wa Yarabawa alkawari ba, to ba kuma za a iya hana wani daga Arewa ya fito takara ba.
“Saboda na san Yarabawan da za su iya mulki. Ba san Ijaw da za su iya. Na san Hausawan da za su iya, kuma har a cikin kabilar Kilba ma na san wadanda za su iya.” Inji Lawan, wanda aka sallama daga aiki bayan kama shi da laifin cinye kudin gwangilar nome ciyawa a Sansanin Masu Gudun Hijira.
“Kai ko ni ko a cikin abokai na akwai wanda zai iya yin shugabancin kasar nan. Duk kuwa da cewa kakaf kabilar mu ba mu wuce matane 300,000 ba.”Inji shi.
Discussion about this post