Babu dalilin da zai sa na fice daga APC –Gwamnan Kogi

0

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya ce har yanzu ya na cikin jam’iyyar APC, saboda babu wani rikici a cikin jam’iyyar a Kogi da har zai sa ya fice ya bar ta.

Bello ya shaida wa manema labarai haka a Fadar Shugaban Kasa, jiya Litinin a wurin taron Kaddamar da Zababbun Gwamnoni da kuma wadanda aka sake zabe karo na biyu.

Ya ce akwai bukatar a kaddamar da zababbun gwamnonin a koya musu makamar aiki, domin a sanar da su kakubalen da ke gaban su.

“To ni dai iyakar abin da na sani a jiha ta, shi ne babu wani rikici a cikin jam’iyyar APC a Kogi.

“Dattawan jam’iyya da sauran masu ruwa da tsakin ta, matasa da bangaren mata da sauran mutane masu mutunci na APC a Kogi duk musul kalau mu ke zaune.

“Wannan zaman lafiya ta tare da rikici ba ne ya sa a zaben shugaban kasa APC ta yi nasara a jihar.

“Mun kuma yi kokarin samun nasarar lashe zaben sanatoci na shiyya biyu daga cikin uku; sannan muka lashe zaben majalisar tarayya bakwai daga cikin mambobi tara.

“A karon farko kuma a tarihin jihar mun yi nasarar lashe zaben majalisar dokoki ta jihar dukkanin 25 din.”

Ya ce wadannan dalilai da kuma wasu da dama sun nuna babu wani rikici a cikin APC a jihar Kogi.

“Don haka masu rara-gefe su na yada maganganu a kai na wai zan bar jam’iyyar APC, to bakin su ya sari danyen kashi.”

Daga nan kuma ya karyata zagin da ake yi masa na almubazzaranci da kudin gwamnati.

Bello ya bugi kirjin cewa gwamnatin sa a cikin shekara hudu ta yi ayyukan da gwamnatocin baya na shekaru 20 kafin shi ba su yi ba.

Ana rade-radin cewa APC ba za ta bai wa Yahaya Bello takara a karo na biyu ba, a zaben gwamnan da za a yi cikin Nuwamba.

Sai dai kuma Bello ya ce babu wata matsala a cikin APC a Jihar Kogi.

Share.

game da Author