AREWA: UNICEF za ta tallafa wa yara 500,000 da ba su zuwa makaranta damar neman ilmi

0

Hukumar Tallafa Wa Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya, wato UNICEF, ta bayyana cewa ta na nan ta na hankoron tattara bayanan kananan yara 500,749 da ba su makaranta a jihohi hudu na Arewa, domin tallafa musu.

UNICEF, ta ce shirin mai suna Ilmantar Da Yara (EAC), za a gudanar da shi ne a cikin jihohi hudu na Arewacin kasar nan, wadanda daga cikin su ne za a zabi yaran da za a rika tallafawa din daga agajin na UNICEF.

UNICEF ta bayyana wannan kokari da ta ke kan yi ne a wani taron kwana biyu da aka gudanar a Kebbi dangane da Shirin Taimakon Dalibai Mata Yin Karatu.

An shigo da tsarin na EAC domin rika samar da tattafin kudaden da za su agaza wa iyayen yara kula da karatun kananan yaran su a jihohin Katsina, Kebbi, Sokoto da kuma Jihar Zamfara daga nan zuwa 2020.

Daga cikin tsarin akwai tura kudade ga masu kula da yara da kuma wasu damammakin samu guraben karatu.

Da ya ke magana a wurin taron, Kodinatan CTP na Jihar Kebbi, Isah Usman, Ya ce sama da yara kanana 31,000 na jihar a halin yanzu ke cin gajiyar naira 8,000 da ake biya wa kowane yaro a zangon karatu daya, domin a agaza wa iyayen sa kula da karatun sa.

Ya ce wannan kuma wata hanya ce ta kara wa yaran kwarin guiwar yin karatu.

“Wannan tsari an shigo da shi ne saboda tallafa wa masu fama da kuncin rayuwa da katutun talauci domin su samu damar kula da karatun ‘ya’yan su.”

Ya ce iyaye musamman mata na yaran ake bai wa kudaden su rika kula da karatun yaran.

Ya ce a shekara kenan ana bai wa kowace naira 24,000 domin daukar dawainiyar yaro da kara masa kwarin guiwar yin karatu.

Ya ce ana sa ran kebe yaro 41,391 tare mata masu kula da su a cikin shekara hudu: Guda 31,044 a Kebbi, sai kuma 10,347 a Zamfara.

“An dauki jihar Kebbi da Zamfara mafi koma baya wajen harkar ilmi, duk kuwa da cewa karatun firamare kyauta ne, kuma tilas ne. Ya ce amma duk da haka, akwai dimbin kananan yaran da ba su zuwa makaranta masu tarin yawa a cikin jihohin.”

Sai dai kuma ya kara da cewa talauci shi ne babban dalilin da ya sa wasu iyaye da dama ba su iya kula da karatun yaran su.

Dalili kenan ya ce a Kebbi za a fara wannan shiri a cikin kananan hukumomi tara, da suka hada da: Argungu, Bagudu, Dandi, Gwandu, K/Besse, Shanga, D/Wasagu, Mayawa da Zuru.

Share.

game da Author