Na jima ina sa idanu akan yanda abubuwa suka fara kasancewa tun daga zaben cikin gida a jam’iyance zuwa kamfe da su zaben gaba daya, da karbar takardar cin zabe da masu fatan alkhairi har zuwa batun zuwa kotu da wasu suka shiga yanzu haka. Abu guda daya da zan furta shine, ko nawa aka siyar da Kare yayi kudi, kuma ba a fadi idan muka kalli siyasar Arewa.
Zaben 2019 bai zo min da mamaki ko kadan ta fuskar cin wasu kujeru ko faduwar wasu ba. Abu guda da ya dauremin kai shine, yanda KUDI ya zama abu na karshe da zai iya tabbatarwa da mutum nasara a zabe duk wani tudu da gangare da za a bi a siyasance. Idan muka yo karatun baya kadan, lokacin da PDP ta yi zaben cikin-gida don futar da wanda zai yi mata takara, sai da irin wannan matsala ta faru, in da a karshe tasirin Dala, ya haddasa zamowar Atiku dan takarar da zai kwafsa da Buhari. Kuma tun daga wannan rana muke da yakinin Buhari ya ci zabe, ko da kuwa bai yi wani kamfe mai karfi ba. Abu na biyu, zarge-zarge sun bayyana sosai akan yanda shi shugaban APC wato Oshiomhole na siyar da wasu kujeru ga wasu mutane haka. Wata kila akan hakane ita APC din ta samu matsala a wasu kujerun gwamnoni da sauransu.
Haka lokacin da kamfen ya fara nisa, Kudin dai shine ya yi karfi sosai wajen yanke yawan farin jinin mutum. Misali, idan kana da hali, za ka iya daukar mutane miliyan guda su zo wajen taronka, a fara baza hotuna ai wane yana da mutane shi zai ci zabe da sauransu. Amma kuma daga karshe, sai ku ga abubuwa sun sauya. Domin da yawan mutane shine cin zabe da wasu ba su fadi zabe a jihohin da suke da iko ko mulka ba, duba da yanda suke hada mutane dubunnai lokacin yakin neman zabe.
Abin da ya sa nake wannan batu shine, ina so na zakulo ribar da Arewa ta samu a zaben ne. Kuma hakan ba zai samu ba, sai mun ga irin wainar da aka soya a lokacin zaben.
Lokacin zabe da hada sakamakon an ga abubuwa a dama da suka faru. Wasu masu dadi ne, wasu kuma ba dadi. A jiha irin ta Kano, tarihi ba zai taba manta irin cin zarafin da aka yi wa Dimokaradiyya ba. A yankin su Gombe da Lagos kuwa, abubuwa ne masu armashi da fahimta. Don kuwa kowa ya ga yanda Ambode ya nuna kishin kasa da biyayyar siyasa ya karbi hukuncin da Tinubu ya yanke masa. Hakanan yanda shi ma Dankwambo ya kuma yin zubar gado da jam’iyyar PDP a Gombe, duk da cewar shi kadai ne ya turje guguwar Buhari ta 2015.
Alhamdulillah. A yau, talakan Arewa zai iya fahimtar bukata da son a yi mulki ta kowacce fuska ita ce burin wani dan siyasa a Arewa, ba wai wani abu ba, idan ka dauke wasu tsirarun jagorori ‘yan kishin Arewar, wanda kowa ya san su.
Batun sunan jam’iyya da manufa babu shi a siyasar Arewa a yau. Duk wanda ka tambaya mecece manufar APC ko PDP, ba zai fada ma ba. Sai dai wata kila a fake da wasu kalamai masu rauni a mizanin tunani. Hakana idan ka kuma tambayar su kan su nagartar ‘yan takarar, shima sam-ma-kal. Don har yanzu da yawa daga cikin wadanda suka ci zaben baya da na yanzu, akan tafiya daya ce kawai ta alfarmar Buhari.
Idan har kuwa an zo kan hakan, to a gaskiya muna cikin matsala da tarin kalubale. A dunkule, kuma a takaice, farashin da ake yi wa delegates da kuma su masu dangwala kuri’a, shine abu mafi hatsari a makomar siyasar Arewa, kuma idan muka kalli hakan sosai, ba wata riba da muka ci a zaben 2019 sai matsaloli.
Idan har za mu yi hakuri mu fadawa juna gasiya, daga 2015 zuwa yanzu, nagartar karatu a Arewa ya bunkasa ne ko ta ragu? Bara, maula da sace-sace da dabanci da jagaliyanci sun karu ko sub ragu? Aikin yi da bunkasa kasuwanci ya karu ko ya ragu? Matasan da ke barin Arewa zuwa Kudu don neman kudi, sun karu ko sun ragu? Lamarin ta’addanci ta fuskoki da dama sun karu ko sun ragu?
Samun nutsuwar amsawa juna wadannan tambayoyi ba tare da jefa ra’ayin siyasa ko bangarenci ba, to ba shakka za mu gane cewar ba bu wata riba da muka ci a zaben nan.
Abu na karshe shine, yanda a yau kuma har zuwa gobe, aka rasa wanda zai iya futowa ya ja al’ummar Arewa a siyasance don ganin an samu ci gaban da ake bukata a zamantakewa. Kowa akwa in da ya sa gaba. Daga malamai zuwa ‘yan kasuwa da ‘yan kwangila gami da barayin ofis, da sauran ya-ku-bayi, kowa akwai alkiblar da ya sa gaba. Da zarar wani ya bawa wasu kudi, sai su futo su kareshi ko su soki wanda ba ya so. Wannan abu shi ya ratsa har kungiyoyin addini da na dalibai gami da ‘yan rajin kare hakkin mutane da sauransu.
Daga karshe, ina kara kira ga matasa, a mike a yi karatu sosai da nazarin halin da duniya take ciki. Mutanen baya da suka yi gwagwarmaya har muke jin dadin muna siyasa a yau da sauransu, to karatu da kokarin da mutanen baya suka yi ne, ba wai ta jagaliyanci da bambadanci suka kwato ‘yancin da muke mora a yau ba.
Akwai aiki mai girma a gabanmu don ganin an fara cin ribar da ta kamata a ci a siyasance a yankin Arewa!