Ana fargabar makomar yaran da Boko Haram suka maida marayu

0

Mazauna sansanonin masu gudun hijira a Jihar Barno sun nuna fargabar yadda rayuwar kananan yara za ta karance, ganin irin yadda suke tashi a sangartacce cikin sansani, ba tare da samun kulawar iyaye ko gwamnati ba.

Dattawan da suka nuna wannan damuwa da fargaba, jiya Litinin tarecda cewa akwai fa fargabar makomar su wadannan yara za ta kasance, idan suka zama matasa, domin ba su da mai sa su abu su yi, kuma ba su da mai hana su har su hannu.

Da ya ke magana da PREMIUM TIMES a daya daga cikin sansanin masu gudun hijirar da ke Kusheri, gefen Maiduguri, Mustapha Tijjani mai shekaru 60 daga Karamar Hukumar Konduga, ya ce akwai akalla akwai kananan yara marayu za su kai 100,000 a sansanoni daban-daban A Jihar Barno.

Ya ci gaba da cewa, “mafin yawa daga cikin su sun zama fandararru, idon su ya bude, kar su ke kallon mutane, saboda sun san abin da ya faru da iyayen su. Su na kuma cike da takaici da haushin irin zaman kunci da kadaicin da suke yi a sansanoni ba tare da kulawa da kaunar da ta kamata su samu aga iyayen su, kamar yadda iyayen sauran yara da Boko Haram bai kashe iyayen su ba ke samu.”

Mustapha ya ci gaba da cewa wadannan yara fa sun kama hanyar zame wa al’umma bala’I idan ba kwakkwaran mataki aka dauka ba, nan gaba sai sun fi Boko Haram zama barazana.”

Mustapha ya nuna wannan damuwa a lokacin da ake nuna wani fim a kan matsalar Boko Haram.

“Wadannan yara fa wasun su an kashe musu iyaye a gaban su, wasu ma yankan rago aka yi wa iyayen a gaban su. Da yawan su ma ba su san daga inda ka kawo su aka jibge a sansanonin Alhazai ba. Wasun su kuma sojoji ne suka karkashe iyayen su a lokacin da ake gumurzu a Boko Haram.

“Ga su nan birjik cikin sansanoni da waje, sai gagaramba su ke yi. Wasu tun sun a jinjirai aka tsinto su aka kawo nan sansani, saboda an karkashe iyayen su, su kuma an bar su da ran su. Wasu yaran kuma sun san daga inda suka fito, amma abin takaici ba su dangin uwa kon na uba a duniya.

“Babu ruwan su da kowa, kuma babu ruwan kowa da su. Za su kwanta barci a lokacin da suka ga dama, sannan su tashi a lokacin da suka ga dama.

Dattijon ya ce a Konduga da shi attajiri ne, amma Boko Haram suka kassara shi, ya koma tantirin talaka.

Share.

game da Author