Ana bukatar sama da malamai mata 58,000 domin inganta ilmin yara mata a Arewacin Najeriya –UNICEF

0

Hukumar Kula da Ilmin Mata ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ta ce akalla ana bukatar karin malamai mata kusan 58,121, wadanda za a yi amfani da su wajen koyar da yara dalibai mata a Arewacin Najeriya.

UNICEF ta ce yin haka zai zama matakin farko domin kokarin cike wawakeken gibin da ke tsakanin yawan dalibai maza yara masu samun ilmi da kuma yara dalibai mata masu samun ilmi a Arewacin Najeriya.

UNICEF ta yi wannan binciken ne cikin 2018 a jihohi takwas na Arewacin Najeriya.

An gudanar da binciken ne domin kokarin inganta yawan kananan yara mata a makarantun Arewacin Najeriya.

Jihohin da aka yi wannan bincike a cikin su, sun hada da Bauchi, Gombe, Katsina, Kebbi, Neja, Sokoto, Taraba da Zamfara.

Wannan shi ne bincike na biyu da UNICEF ta yi a Shirin ta na 3 don Kara Yawan Dalibai Mata a Arewacin Najeriya.

An gabatar da wannan sakamakon bincike ne ga wani taron kara wa juna sani da aka gudanar jiya Laraba a Abuja.

An gudanar da binciken ganin yadda aka samu sama da kananan yara milyan 12 da ke gagararamba a Arewa ba tare da zuwa makaranta ba.

An ce malamai mata na da muhimmiyar rawa wajen bai wa kananan yara mata kwarin guiwar daurewa su yi karatu.

Binciken ya kara nuna cewa akwai karancin malamai mata a makarantun firamare masu tarin yawa a Arewa.

Daga nan aka nuna cewa sai an tashi tsaye an nunka yawan malamai mata har nunki hudu, wato zuwa 58,121 kafin a samu ingantaccen ci gaban ilmantar da yara mata kanana a Arewa.

Jami’in tuntuba na UNICEF, mai suna Noel Ihebuzor ne ya gabatar da wannan bincike, tare da yin kira ga gwamnati da ta mike tsaye domin ilmantar da kakanan yara mata masu tarin yawa a Arewa.

Share.

game da Author