An yi garkuwa da wasu manyan Jami’an Hukumar Agajin Gaggawa (NEMA) su hudu a Jihar Ribas.
An bayyana cewa dukkan su manyan jami’ai ne da aka arce da su bayan an bindige wani daya daban.
Lamarin ya faru ne Karamar Hukumar Abua-Odua, a lokacin da jami’an ke kan gudanar da aikin su.
Jami’an sun hadu da wannan ibtila’i a lokacin da suke aikin daukar sunayen wadanda ambaliya ko rikici ya shafa, domin NEMA ta ba su agajin kudaden noma.
An ware kudaden ne domin amfanar jihohi 18, kuma Ribas ta na cikin su.
Cikin wadanda aka tsere da su din har da mace wadda ta rigaya ta kammala aikin tantance wadanda aka dauki sunayen na su. Sauran ukun kuma maza ne.
Sai dai kuma rahotanni sun ce jami’i daya ya tsare da kyar, ba a samu damar damke shi ba.
Ya samu nasarar tsrewa ne, amma an harbe shi a kafa.
An ce yanzu haka ana kula da shi a wani asibiti da ba a ambaci sunan sa ba.
An kasa samun Daraktan NEMA Mustapha Maihaja domin jin karin bayani daga gare shi.