Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas Bala Elkana ya sanar cewa an yi garkuwa da darektan hukumar kashe gobara na jihar Rasaki Musibau da wasu mutane shida.
Elkana ya fadi haka ne wa manema labarai ranar Lahadi a garin Legas.
Ya ce masu garkuwa da mutane sun sace Musibau da wasu mutane shida da karfe takwas na yamman Asabar a kan gadan Iwoye dake hanyar Itoikin-Epe a Ikorodu jihar Legas.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zubairu Mu’azu ya yi tir da haka sannan ya ce rundunar ta fara bin sawun wadannan mutane domin ceto mutanen da aka sace.
” Mufutau Adams manajan hukumar kashe gobara na jihar, Mrs Funmilayo Adelumo, Asiogu Martha, Lasisi Muka da wasu mutane biyu na cikin wadanda aka sace a ranar Asabar sannan an tsinci motoci masu kira irin ta Toyota Sienna, Toyota Corolla da Opel Jeep a kan gadar da aka sace wadannan mutane.”
Mu’azu ya ce domin samar da tsaro da kuma ganin an taso keyan masu garkuwa da mutane rundunar ta hasafa tsaro a manyan titunan Itoikin-Epe road, Ketu, Ereyun da sauran manyan titunan dake jihar.
Discussion about this post