An sake damke mata 70 a gidan tambele a Abuja

0

Jami’an ’Yan Sandan Abuja sun sake kai farmaki a gidajen rawa da tambele a Abuja, inda suka cafke mata 70.

Makonni biyu da suka gabata aka fara kai wannan farmaki inda aka kama mata 30.

Wannan sabon kame da aka yi shekaranjiya Asabar, an tarkata dukkan wadanda aka kama, aka kulle caji-ofis na ’yan sanda.

Martin lauya mai suna Martin Obono, ya ce a gaban sa aka kawo su ofishin ’yan sanda na Utako, ranar Asabar da dare.

Ya ce an zargi wasu matan da laifin karuwanci. Ya kuma yi zargin cewa wasu matan ma sai da jami’an tsaro su ka ci zarafin su ba da amincewar su ba.

Kafin ya shaida wa PREMIUM TIMES haka, sai ma da ya rigaya ya watsa a shafin sa na twitter, inda ya ce:

“A yayin da na ke rubutun nan, yanzu haka an kamo mata 70 an kawo su ofishin ’yan sanda na Utako. Wadannan na daban ne, banda wadanda aka kamo aka tsare a ranar Juma’a da dare.

“Laifin su shi ne an same su a gidan rawa, wasu kuma an zarge su da karuwanci. Wasu an ci zarafin su, har ma an ji musu ciwo a farjin su.

“Daya daga cikin matan ma har da dan ta mai watanni biyu da haihuwa aka tsare. An hana ta shayar da jinjirin, duk da rokon da ta ke ta yi ta na kuma rusa kuka. Har sai da wata mace ’yar sanda ta kira DOP ta shaida masa, sannan aka kyale ta, ta shayar da dan na ta.

“Ana zagin jami’an ‘task force masu kamen su na cin zarafin matan. Wasu ma har sai da suka nuna ciwon da aka ji musu jini na zuba a cikin al’aurar su.” Haka Obono ya rubuta a shafin sa na twitter.

Duk da cewa an haramta karuwanci a Abuja, jami’an tsaro na amfani da wannan damar su na cin zarafi tare da tozarta matan da su ke kamawa.

Sun fi bi su na kamen wadanda ke yawo da dangalallun kaya, fan-darin-ka-tsirara.

Ko da samame suka je a gidajen tambele, rawa ko tambada, ba su cika kama maza ba, sai dai mata.

Duk da yawan rahotannin da ake kaiwa korafe-korafen cin zaramin al’aurar mata da ake yi, har yau ba ta kafa wani bincike ba.

Share.

game da Author