An sace Baturen Scotland da Ba’Amurken Canada

0

Abokan aiki da abokan zaman gidan wani Ba’Amurken Canada da Baturen Scotland, sun tabbatar da sace su biyun.

Wadanda aka yi garkuwar da su, an tabbatar da cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da su a daidai wurin aikin wata rijiyar danyen man fetur a Abua, cikin Jihar Rivers.

Gamayyar jami’an tsaro na JTF da aka tura yankin Neja-Delta domin kula da tsaron rijiyoyin mai sun tabbatar da sace Turawan su biyu a jiya Lahadi.

Wadanda akadai an ce sun a aiki ne a wata rijiyar mai da aka ce NDPR ke gdanar da ayyuka a wurin.

Rijiyar an gina ta ne a Karamar Hukumar Abua-Odua, mai arzikin danyenn man fetur a Jihar Rivers.

Kakakin JTF na yankin, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da sace Turawan a Yankin Neja Delta.

Ya ce zaratan JTF na bakin kokarin ganin sun gano inda aka arce da su, kuma sun kwato su da ran su.

Daga nan sai ya shawarci dukan kamfanonin hakar danyen mai a yankin Neja Delta da su tanaji isasshen tsaro ga ma’aikatan da ke musu aiki a rijiyoyin mai.

Share.

game da Author