A wani samame da jami’an tsaro suka kai gidan rawa da shakatawa dake unguwar Utako, babban birnin tarayya Abuja mai suna Caramela, an kama mata akalla 35 dake yin rawa tsirara a gidan.
Wannan kame dai an yi shi ne ranar Laraba.
Hukumar kula da garin Abuja AEPB da jami’an tsaro suka kai wannan samame gidan shakatawar.
Umar Shu’aibu da ya jagoranci wannan hari ya bayyana cewa an dade ana kawo karar wannan gidan rawa da shakatawa ga hukumar AEPB.
” Bayan mun saurari koke-koken mutane da mazauna wannan unguwa sai muka fara bincike akai.
Bayan haka Salisu ya ce an rusa katangar dake gaban wannan wurin shakatawa domin tun asali filin ba an bada shi don a gina gidan rawa bane. Asibiti ne ya kamata a gina a wannan wuri.
“A ranar da muka afka wannan gida sai muka taras da mata suna rawa a gaban jama’a tsirara. Daga nan sai tarkata su duka inda yansu haka suna Asibiti ana duba inda daga nan za a mika gidan inda ake gyara tarbiyyar yara gagararru shar na tsawon wata uku.
Sakataren hukumar SDC dake Abuja ta ce duka matan da aka kama ya’yan attajiran Abuja ne sannan wasunsu ma matan aure ne.