Jami’an ’Yan Sanda sun bada sanarwar ceto wasu ’yan Chana biyu da aka yi garkuwa da su a ranar Laraba, a Jihar Ebonyi.
Kakakin Jami’an Tsaro na jihar, Loveth Odah, ta bayyana wa manema labarai haka a jiya Lahadi, a Abakalili, babban birnin Jiar Ebonyi.
Ta ce yayin da wadanda suka yi garkuwar da su suka ga jami’an tsaro sun kure musu gudu, tilas ta sa suka gudu suka bar wadanda suka yi garkuwar da su a cikin kungurminn daji.
“An ceto su wajen karfe 11 na safe. Sun masu garkuwa sun gudu sun bar su, bayan da suka ga an kusa ci musu. Sai suka bar su a cikin dokar daji, su kuma suka tsare.”
Loveth ta kara da cewa ba a doke su ko jikkata su ba, amma dai ba za a ce ba su cikin halin damuwa ba.
Ta yi kira bakin ‘yan kasashen waje da ke jihar da su rika hada kai da jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin a rika kiyaye lafiyar su kawai.
Ta kara da cewa rundunar yan sandan jihar ta kira taro da baki ‘yan kasar waje taron gaggawa domin tattauna batun tsaron su.
An dai sa ce wasu ’yan bindiga ne sanye da hular da ke rufe fuskokin sa su da huluna suka sace ’yan kasar Chana su biyu din ne, wato Sun Zhixin da Quing Hu a wurin wani aiki cikin Karamar Hukumar Ohoazara ta jiyar Ebonyi.
Sunan kamfanin da suke aiki Tongyi Construction Company.
Discussion about this post