Manyan jam’iyyar APC biyu na Yankin Kudu maso Kudu, Rotimi Amaechi da Godswill Akpabio sun hadu, kuma sun dinke barakar da ke tsakanin su.
Kakakin jam’iyyar APC ne ya bayyana haka jiya Litinin, bayan haduwar tsofaffin gwamnonin na Ribas da kuma Akwa Ibom.
Su biyu sun rike jihohin su tsaron shekaru takwas zuwa 2015.
Daga nan Amaechi ya koma APC, aka nada shi Ministan Harkokin Sufuri, shi kuma Akpabio ya ci zaben sanata, ya zama Shugaban marasa rinjaye.
Kakakakin Kamfen din Shugaba Muhammadu Buhari, Festus Keyamo ne a jiya Litinin ya bayyana ganawar ta su a ranar Lahadi da dare.
Ya ce sun hadu a gidan jagoran APC, Nasiru Danu a Abuja, aka sasanta su a bisa neman yin hakan daga Akpabio.
Danu na daya daga cikin daraktocin kamfen din Buhari a zaben 2019.
Dukkan su dai Amaechi da Akpabio, bayan sun koma APC, sun kasa samun nasara a jihohin su na Ribas da Akwa Ibom.
Yayin da Kotun Koli ta hana APC shiga kowane zabe, in banda na shugabann kasa a Ribas, kokarin da Amaechi ya yi na hada karfi da wata jam’iyya domin a kayar da PDP ya ci tura.
Shi ma Akpabio, baya ga cewa PDP ce ta yi nasarar zaben gwamna, hatta kujerar sa ta sanata ya kasa yin nasara, inda a yanzu ta fada hannun PDP, jam’iyyar da ya fice cikin 2018 ya koma APC.
Su biyun sun tattauna ne dangane da kokarin dinke barakar su, wadda ta faru tun a lokacin zaben Shugaban Gwamnonin Najeriya, cikin 2011 zuwa 2015.
Sun kuma tattauna yadda za su sake farfado da APC a yankin su, domin tunkarar nasarorin da za su nema a gaba.
Daga nan kuma sun amince sun manta da duk wani sabani da ya taba faruwa a baya. Sun ce yanzu duk ya zama tarihi, an wuce wurin.