Ali Nuhu Da Adam A. Zango Nasiha Suke Bukata Ba Zuwa Kotu Ba, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Ba zuwa kotu bane hanyar warware matsalar da take tsakanin Ali Nuhu Muhammad da Adam A Zango ba. Kotu ba zata iya warware matsalarsu ba din-din-din idan har basu ji tsoron Allah sun ajje hassada da hamayya ba.

Gaskiya fa duk sanda mutane biyu suka hadu akan soyayyar abu guda daya sun zama maqiyan junansu kamar yadda Thomas Hobbes yace.

Idan zamu duba maganar wannan masanin zamu gane cewa rikicin Kannywood ba zai ta6a sauki ba idan basu daina tseren mallakar sarautar kannywood ba. Ko wanne daga cikinsu baya so dan uwansa ya fishi ‘stardom’. Wannan stardom din itace take bayyana kar6uwarka a wajen masu kallo.

Mu bamu da burin mu yi ta rubuce rubuce akan abu daya amma ya zama dole ne.

Ku yi hakuri kuyi yaki da shaidan, komai a hannun Allah yake, shine yake yin yadda yake so ga wanda yake so. Ba lallai bane don kafi mutum yau kuma gobe ma ka fishi, hakazalika don ka fara samun daukaka; ba daidai bane ka raina mutumin da shine silar cigabanka.

Ina basu Shawara, kada su saki fuska shaidanun mutane su Kara wa sabanin nasu tsanani. Sanin kansu ne yanzu an daina yayin irin wannan hamayyar. Babu wani alheri a cikinta, hasali ma saidai ta shigo muku da munafikai su yi ta yawo a tsakaninku.

Allah ya jikan Albani Zaria, a cikin wani Kaset dinsa mai suna “Farin sakon fatan alheri ga kungiyar izala 2” ya karanto wani hadisin Annabi (SAW) da yake cewa an ta6a dauke saukar daren lailatul qadr saboda wasu musulmai guda biyu suna gaba.

Wannan nasiha ce ga kowani musulmi da yake gaba da dan uwansa. Babu magani mai ci da sauri kamar hakuri, dole ne su yi hakuri su zauna da junansu lafiya, ina basu shawara ne a matsayinsu na musulmai ‘yan uwanmu.

Tabbas mun hadu a addini, kalmar shahada ta mayar damu yan uwan juna. Babu buqatar sai mun san juna, ba shine matsalata ba, mafita ake nema musu a matsayinsu na masu sana’a daya kuma suke nema su ci mutuncin juna har da zuwa kotu.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author