Akwai Matsala Idan Aka Sallami Matasan Da Suke Cikin Tsarin Npower, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Babu kasar da zata cigaba idan bata yi amfani da matasanta wajen samar da kuzarin ginata ba.

Bincike ya bayyana cewa, matasan da suke kasa da shekara arba’in sun bayar da gudunmuwa tukuru wajen cigaba a duniya ta kowane bangare da ya shafi kimiya, fasaha, siyasa da tattalin arziki.

Idan muka gwada matasan Najeriya da wadannan matasan da duniya take alfahari dasu zamu tabbatar da cewa matasan kasarmu basu samu wannan damar ba saboda talauci da halin ko in kula daga gwaunati.

Cikin ikon Allah, mun gode wa Allah, tun daga zuwan Shugaba Buhari a shekara ta 2015 ya samar da tsarin Npower saboda ya samar wa da matasa aikin yi na wucin-gadi.

Mustapha Soron Dinki

Mustapha Soron Dinki

Tabbas anyi nasarar daukar matasa dubu dari biyar (500,000) a cikin wannan tsarin domin su yi aikin shekara biyu suna Kar6ar tallafin dubu talatin 30k, kuma mun gode sosai saidai muna tausayin yadda rayuwar wadannan matasan zata kasance idan aka sallamesu bayan sun saba da kar6ar dubu talatin a wata.

Abubuwan da ka iya faruwa idan aka sallami wadannan matasa sune:-

– Za a samu rabuwar aure da yawa saboda wasu suna da aure don dan Adam baya iya rayuwa ba aure.

– Na biyu kuma za a samu yunwa da fatara domin wasu daga cikin ‘yan Npower sun dora rayuwarsu da ta iyayensu akan naira dubu talatin.

– Na uku kuma dole a samu faduwar tattalin arzikin matasa saboda wasu biyan bashi suke biya da kudinsu.

Wadannan matasa sun samu canjin rayuwa akan rayuwarsu ta baya bayan kammala jami’a shekaru da yawa.

Lallai yanzu sun saba da kudi don haka akwai matsala idan aka mayar dasu rayuwarsu ta baya. Hakan zai iya haifar da komai duba da yadda bakin ciki da talauci yake haifar da laifuka.

Muna rokon gwaunatin Najeriya ta taimakawa wadannan matasa. Kodai a daukesu aiki, ko kuma a cigaba da tsarin dasu.

Allah ya taimaka.

Share.

game da Author