Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya bayyana cewa ya garzayo fadar shugaban kasa ne domin ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari bayanin abubuwan da suka faru dalla-dalla a zaben jihar da har yanzu ba a iya mika masa shaidar zaben sa da aka yi ba.
Idan ba a manta ba, jam’iyyar APC ta dakatar da shi Okorocha da gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun daga jam’iyyar a bisa zargin yi wa wata jam’iyya aiki.
Bayan haka hukumar zabe ta ki mika wa Okorocha shaidar tabbatar masa da yin nasara a zaben a cewa akwai korafe-korafe a kan zaben sa da ya hada da tilasta wa malamin zabe ya bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan shiyyar sa a jihar.
Da yake zantawa da manema labarai a bayan ganawar da suka yi a asirce, Okorocha ya ce bayan bayyana wa Buhari yadda a ka gudanar da zaben sa ya roke shi da ya ziyarci jihar domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da ya aiwatar a jihar.
” Babu yadda za ace wai an tilasta wa malamin zabe ne kafin ya bayyana sakamakon zabena. Na farko dai ba a gidansa ko gidana aka yi ba. A bainar jama’a ya fadi sakamakon zaben. A gaban Jami’an tsaro.
” Saboda haka ina nan ina jira, har lokacin da hukumar zabe zata mika mini shaidar nasarar zabe na.
” Bayan haka munyi ayyuka da dama a jihar Imo da ba a taba yin irin wadannan ayyuka ba. Duk sune muke so Buhari ya zo ya kaddamar da su.
” Akalla muna da ayyuka da muka yi sama da 1000 da Buhari zai kaddamar idan ya zo jihar Imo.
” Akwai Asibitoci, titunan, Makarantu, Kasuwanni, cibiyoyi da sauran su.