Akalla mutane miliyan 4 ne ke fama da matsanancin Talauci a jihar Kano

0

Shugaban sashen kasuwanci ‘ Dangote Business School’ dake jami’ar Bayero dake jihar Kano Murtala Sagagi ya bayyana cewa akalla mutane miliyan 4 ne ke fama da bakar talauci a jihar.

Sagagi ya bayyana haka ne da yake jawabi a taron kungiyar masu ruwa da tsaki na jihar Kano ranar Asabar.

” Rashin maida hankali wajen farfadowa da gina ayyukan ci gaba a jihar da gwamnatocin da aka yi a jihar basu yi ba, da malamai da su kansu mutanen jihar yasa aka kasa warware wannan kulli da ya dabaibaye mutanen jihar na bakar talauci.

” Akalla masana’antu 500 ne suka durkushe a jihar Kano a dalilin rashin samar da manufofin da zasu taimakawa jihar wajen farfado da irin wadannan kamfanoni. Sannan kuma har yanzu gwamnatin jihar Kano bata iya saita harkokin ayyukan gona ba ta yadda za a iya samun waraka a jihar.

Shi ko Aliko Dangote kira yayi ga gwamnati da ta maida hankali wajen ganin ta inganta samar da wutan lantarki a kasar nan cewa kamfanoni da yawa sun durkushe ne saboda fama da rashin wutan lantarki.

Ya ce ko da yake gwamnati kawai ba za ta iya samar da wadannan abubuwa ita kadai ba, ya ce ” Dole ne gwamnati ta maida hankali wajen ganin ta samar wa mutane yanayi mai nagarta da kowa zai iya sakhannun sa cikin harkokin kasuwanci da sana’ a a kasar nan.

Bashir Tofa, wanda shine shugaban wannan kungiya kira yayi ga masu ruwa da tsaki a jihar da su maido hankulansu wajen gani an samar da hanyoyin da za a kubutar da jihar daga wadannan matsaloli da take fama da su.

A nashi jawabin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kira yayi ga shugabannin wannan kungiya da su samar da hanyoyin da za a rika tsawata wa masu neman lalata ganuwar Kano.

Sarki Sanusi ya ce yanzu an maida ganuwar kasuwa. Ko ina ka bi zaka ga mai tireda a jikin ganuwar.

Ya kuma kara da cewa dole a maida hankali wajen lalacewar tarbiyyar matasa musamman matsalar shaye-shaye. Daga nan kuma sai yayi kira da a duba matsalar yadda maza ke sakin mata a jihar.

” Masarautar Kano za ta mika kudiri majalisar dokoki na jihar game da yadda ake sakin mata da kuma tarbiyyar ya’ya.”

Share.

game da Author