Akalla mutane 21 ne mahara su ka kashe a Kaduna

0

A wani sabon hari da wasu mahara suka kai kauyukan Banono da Angwan AKU dake gundumar Kufana, Karamar hukumar Kajuru a kan babura, sun hallaka mutane 21 sannan mutane uku sun tsira da raunuka.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo ya bayyana cewa baya ga mutane da suka ka kashe mahjaran sun sace shanu har guda hamsin.

Sabo ya ce maharan sun kai harin ne da misalin karfe 9:30 na safiyar Litinin a kan babura inda suka rika harbi ko ta ko ina. Sun cinna wa gidaje da dama wuta.

Bayan haka ya kara da cewa jami’an ‘yan sanda da wasu ‘yan bangan wadannan kauka ne suka fatattaki maharan.

Tuni dai a garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna matukar bacin ran sa bisa ga abubuwan dake faruwa a kasar nan musamman Arewacin Najeriya.

A takarda da kakakin sa, Garba Shehu ya saka wa hannu, Buhari ya roki sarakuna da shugabnnin anguwanni da su rika kwaban mutanen yankin su da nuna musu illar komai ace sai an rama shi.

Buhari ya kara da cewa yin haka ba dai-dai bane domin tarwatsa zaman tare da muke da juna yake yi.

Share.

game da Author