Aisha Buhari za ta gina jami’ar ‘Muhammadu Buhari’

0

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari za ta gina jami’a mai suna ‘Jami’ar Muhammadu Buhari’.

Aisha ta bayyana haka ne a garin Yola inda ta ce za ta hada guiwa da kasar Sudan da Qatar wajen gina wannan jami’a.

Sai dai bata fadi ko a ina zata kafa jami’ar ba.

A wajen taron manyan baki da suka halarta sun yi jawabai kan matsaloli da dama da mutanen jihar ke fama da su.

Umar Abubakar yayi jawabi kan tsaro da ake fama da shi, Buba Marwa kan illar shaye-shayen kwayoyi, Sanata Silas Zwingina kan inganta ayyukan gwamnati sannan Dr Umar Bindir yayi jawabi ne kan matsanancin talauci da ake fama dashi.

Share.

game da Author