Adam Zango ya dage auren sa sai bayan Sallah

0

Fitaccen jarumin Kannywood Adam Zango ya sanar da dage auren sa da ya shirya yi da sabuwar amaryan sa Safiya sai bayan Sallah.

Zango ya bayyana haka ne a shafin sa ta Instagram ranar Talata.

Idan ba a manta ba Zango yayi ta saka wa a shafin sa ta Instagram cewa zai auri Safiya sabuwar amaryar sa ranar 25 ga wannan wata wato ranar Juma’an nan.

Zango ya rika fadi da nuna sabon gidan sa da ya gina ya na ta zumudin cewa wannan gida ta sa ce da sabuwar amaryarsa.

Bincike da aka yi, wannan aure da Zango zai yi itace ta shida cikin jerin aurarrakin da yayi.

Zango baya tare da kowacce mata yanzu haka domin kuwa ya saki dukkan su.

Ta karshe itace Ummukhulsum da ya auro daga kasar Kamaru.

Kafin su rabu ya rika saka hotunan ta da shi a shafin sa ta Instagram yana bayyana irin jin dadin zama da ita da yake yi.

Ummukhulsum ta haifa masa ‘yar sa ta farko da ya rada mata suna Murjanatu.

Sai dai kuma wani makusancin Adam Zango ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ba zai iya magana game da bikin ko daurin aurin ba. Yana mai cewa ba su ma so kowa ya san me ake ciki game da abin.

Da aka tambaye shi game da wadanda ke bukatan halartar bukin fa, yaya za su yi, sai ya fadi cewa ba su gayyatar kowa a wannan daurin aure. Sannan ya katse waya.

Sannan shi kansa Zango din ya cire wannan sako na daga auren da yayi a shafinsa ta Instagram.

Share.

game da Author