Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin cewa a gaggauta maida asibitin cikin Fadar Shugaban Kasa ya rika gudanar da ainihin aikin da aka ce shi zai rika yi.
Kamar yadda wani babban jami’i a fadar shugaban kasa ya bayyana, ya ce dama can an gina asibitin ne domin kula da lafiyar iyalan Shugaban Kasa da na Mataimakin sa da ma’aikatan fadar shugaban kasa.
Jalal Arabi, Babban Sakatare na Fadar Shugaban Kasa ne ya bayyana haka a yau Litinin a Abuja, a lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan batun Kasafin Kudi.
Arabi ya kara da cewa tunanin hana kowa zuwa asibitin sai iyalan Shugaban Kasa da na Mataimakin sa, da ma’aikatan gidan gwamnatin ya fito ne daga Ofishin Shugaban Kasa shi kan sa.
Ya ce an yi hakan ne domin a tabbatar asibitin ya na yin aikin da ya kamata ta yadda wadanda aka gina shi domin su za su rika cin moriyar sa.
Bayan ya kammala kare kasafin kudin da asibitin zai ci, sai Arabi ya fayyace wa manema labarai cewa tunanin maida Cibiyar zuwa wurin duba lafiyar iyalan Buhari da na Osinbajo, ya zo ne domin a rage kashe makudan kudade a asibitin. Ya ce za a rika yin ‘daidai-kurji-daidai-ruwan sa.’
Ya ce yawan dimbin jama’ar da ke halartar asibitin ke kawo kalubalen da a ke fuskanta. Domin ba don su aka yi asibitin ba.
Sannan kuma ba a cajin kowa ko kwabo, da kudin da ake ware masa a kasafin kudi kadai ake tafiyar da shi.
Sai dai kudaden da ake warewa kadai ake tafiyar da asibitin. Idan mara lafiya ya zo aka ba shi maganin da ya yi saura, ya kasance babu ko kwayar magani daya, to haka za a zauna zaman jira babu magani, har sai lokacin da aka sakar wa asibitin kudi kuma.
“Amma sabon tsarin yanzu shi ne za a maida shi zuwa wurin duba lafiyar iyalin shugaba da na mataimakin sa kadai, tunda dama don su ne aka gina shi.
Idan ba a manta ba, a cikin 2017 uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta je asibitin domin a duba lafiyar ta, amma ta samu ko sirinji daya babu a asibitin.
Daga nan Buhari ya ce a yi bincike.
Cikin 2016 PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa kudaden da ake warewa asibitin a duk shekara sun zarce wadanda ake Manyan Asibitocin Koyarwa na kasar nan guda 16.
Sai dai kuma su masu kula da asibitin sun jajirce cewa tsakanin 2015 zuwa 2017, naira bilyan 1.2 kadai asibitin ya karba domin sayen magunguna da sauran ayyukan yau da kullum.
Arabi ya ce an ware wa asibitin kasafin naira bilyan 1.03 a 2018.
Shugaban Kwamitin, Sanata Danjuma La’ah, na PDP daga Kaduna ta Kudu, ya goyi bayan matakin da aka dauka na maida asibitin zuwa kula da wadanda don su ne kadai aka gina shi.
Discussion about this post