Ya zuwa yanzu dai an kammala zaben gwamnoni, har ma da inda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce zabe bai kammalu ba.
Abin da ya rage kawai shi ne a ga yadda za ta kaya a Kotunan Sauraren Kararrakin Zabe, inda wasu gwamnonin za su tsira, wasu kuma za su ga samu sannan kuma su ga rashi.
Sakamakon zabe ya nuna cewa Jihohi biyar da aka sake kirga da wadanda aka maimaita zabuka a wasu yankuna, duk PDP ce ta lashe zabukan.
Wadannan Jihohi sun hada da Adamawa, Benuwai, Taraba, Ribas, Sokoto. Sai kuma jihohin Kano da Filato ne su biyu APC ta yi nasara kenan.
Gaba daya dai APC ta lashe jihohi 15, ita kuma PDP ta lashe 14 a zaben gwamna da aka gudanar.
An yi zaben gwamna a Osun cikin 2018, haka ma a jihar Ekiti. Za a yi na jihar Anambara cikin wannan shekara tare da na Ondo da Bayelsa.
Zaben 2019 ya nuna cewa PPD ta samu karin jihohi, yayin da APC ta yi asarar jihohi.
A lokacin da aka shiga zabe, APC na rike da jihohin: Kebbi, Jigawa, Zamfara, Kano, Adamawa, Katsina, Bauchi, Kaduna, Borno, Yobe, Niger, Ogun, Plateau, Lagos, Nasarawa, Oyo da Imo.
Bayan kammala zabe, APC ta yi asarar jihohi hudu, da suka hada da: Bauchi, Oyo, Adamawa and Imo.
Sannan kuma Kotun Daukaka Kara ta soke nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaben gwamnan jihar Zamfara, inda kotun ta jajirce cewa bai dace APC ta shiga zaben ba.
A halin yanu dai ana sauraren hukuncin da Kotun Koli za ta yanke.
Haka abin ya ke a jihar Osun, Kotun Daukaka Kara ta soke nasarar da APC ta samu, ta ce a bai wa PDP, amma kuma APC ta garzaya Kotun Koli. Ana jiran hukunci na karshe kenan a jihar Zamfara da Osun.
A na ta bangaren, PDP ta shiga zabe ta na rike da Jihohin Gombe, Enugu, Abia, Kwara, Cross River, Delta, Sokoto, Akwa-Ibom, Ebonyi, Benue, Rivers da Taraba.
Bayan kammala zabe, PDP ta yi asarar Gombe da Kwara kadai.
Idan har PDP ta kwaci Kano, Zamfara da Osun a Kotu daga hannun APC, zai kasance ta na da jijohi 17 kenan ita kuma APC na da 12 daga cikin jihohi 29 da aka yi zabe a 2019 kenan.
Idan aka hada da jihohin da ba a yi zaben 2019 tare da sub a, APC na da jihohi 20 kenan ita kuma PDP ta na da 15.
APC ke da Ondo, Edo, Osun, Kogi da Ekiti a cikin jihohin da ba su yi zaben 2019 ba. ita kuma PDP ta na da Bayelsa, sai APGA mai Jihar Anabra tal.
Za a gudanar da zaben gwamnan Kogi da Bayelsa cikin 2019. Ondo da Edo kuwa cikin 2020; Anambra cikin 2012; Osun da Ekiti cikin 2022.
Ga yadda sakamakon zaben gwamna na kowace jiha ya kasance a cikin jihohi 29 da aka gudanar da zaben 2019:
Abia
PDP 261,127
APC 99,574
Adamawa
PDP 376,552
APC 336,386
Akwa Ibom
PDP 520,163
APC 172,244
Bauchi
PDP 515,113
APC 500,625
Benue
PDP 434,473
APC 345,155
Borno
APC 1,175,445
PDP 66,215
Cross River
PDP 381,484
APC 131,161
Delta
PDP 925,274
APC 215,038
Ebonyi
PDP 393,049
APC 135,903
Enugu
PDP 449,935
APC 10,423
Gombe
APC 364,179
PDP 222,868
Imo
PDP 273,404
AA 190,364
Jigawa
APC 810,933
PDP 288,356
Kaduna
APC 1,044,710
PDP 814,168
Kano
PDP 1,024,713
APC 1,033,695
Katsina
APC 1,178,868
PDP 488,705
Kebbi
APC 673,717
PDP 102,625
Kwara
APC 331,546
PDP 115,310
Lagos
APC 739,445
PDP 206,141
Nasarawa
APC 327,229
PDP 184,259
Niger
APC 526,3
PDP 298,056
Ogun
APC 241,670
APM 222,153
Oyo
PDP 515,621
APC 357,982
Plateau
APC 562,109
PDP 559,437
Rivers
PDP 886,264
AAC 173,859
Sokoto
PDP 512,002
APC 511,660
Taraba
PDP 520,433
APC 362,735
Yobe
APC 444,013
PDP 95,803
Zamfara
APC 534,541
PDP 189,452.