Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Edo David Osifo ya bayyana cewa gwamnatin jihar na kokarin kara yawan asibitocin kula da masu fama da zazzabin lasa domin rage matsalar yawan cinkoso da ake samu a asibitin Irrua dake jihar.
Osifo ya sanar da haka ne ranar Laraba a garin Benin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.
Idan ba a manta ba rahotannin hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ya nuna cewa jihar Edo ce ta fi fama da cutar a kasar nan.
Bisa ga rahotan mutane 184 ne suka kamu da cutar sannan 29 sun rasu jihar.
Osifor ya kara dacewa gwamnati ta bude fannin kula da masu dauke da zazzabin lasa a asibitin Stella Obasanjo sannan gwamnati na gab da kammala gina wani asibitin a Auchi.
Ya kuma jero hanyoyin da mutane za su kiyayewa domin gujewa kamuwa da cutar:
1. Da zaran mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.
2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.
3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci nesa da fitsari da kuma kashin beraye.
5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi.
Discussion about this post