Gwamnatin jihar Ondo ta bayyana cewa ta kan kashe tsakanin Naira miliyan 1.6 zuwa 1.5 a kan duk mutumin da ya kamu da zazzabin lassa a jihar.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Wahab Adegbenro ya sanar da haka wa manema labarai a garin Ondo inda ya kara da cewa gwamnati ta kashe wadannan kudade ne tsakanin watannin Janairu zuwa Fabrairu 2019.
” Tun da cutar ta bullo a wannan shekarar mutane 115 ne suka kamu da cutar inda daga ciki 21 suka mutu.
” Cutar ta bullo a kananan hukumomin Owo, Ose, Akoko ta Arewa da kauyukan dake kusa da jihar Edo.
Adegbenro yace bashi da masaniya game da adadin yawan mutanen da gwamnati ta kashe wa wadannan kudade amma yana tabbatar da cewa gwamnati na iya kokarinta wajen ganin ta dakile yaduwar cutar.
Ya kuma yi kira ga gidajen jaridu da masu ruwa da tsaki a jihar kan hada hannu da gwamnati wajen wayar da kan mutane game da cutar.
‘‘Babbar matsalar da muke fama da shi yanzu haka shine wayar da kan mutane game da mahimmancin tsaftace muhallinsu ganin cewa mutane da dama na zama cikin kazanta wanda haka na cikin hanyoyin kamuwa da cutar.
Wale Oke shugaban kungiyar likitocin Najeriya na jihar (NMA) a nashi tsokacin ya yi kira ga mutane da su gaggauta zuwa asibiti a duk lokacin da basu gane jikinsu ba domin haka na taimaka wa waje hana yaduwar cutar.
‘‘Rashin zuwa asibiti da wuri da shan magani ba tare da izinin likita ba na daga cikin matsalolin da ya sa mutane ke rasa rayukan su a dalilin kamuwa da cutar.
Ya kuma jero hanyoyin guje wa kamuwa da cutar kamar haka;
1. Da zarar mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.
2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.
3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci nesa da fitsari da kuma kashin beraye.
5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi.
Discussion about this post