ZAZZABIN LASSA: Adadin yawan mutanen da suka rasu ya 93 a Najeriya – NCDC

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa an sami karuwa a yawan adadin mutanen da suka rasa rayukan su a dalilin kamuwa da zazzabin lassa a Najeriya.

Wannan abin tashin hankali ya faru ne a tsakanin watannin Janairu zuwa Maris.

Ihekweazu yace daga watan Janairu zuwa Maris hukumar ta yi wa mutane 3,1374 gwajin cutar, daga cikin su 420 sun kamu da cutar sannan mutane 93 sun rasu a dalilin kamuwa da cutar.

An samu barkewar cutar a kananan hukumomi 66 dake jihohi 21 da suka hada da Edo, Ondo, Bauchi, Nasarawa, Ebonyi, Plateau, Taraba, FCT, Adamawa, Gombe, Kaduna, Kwara, Benue, Rivers, Kogi, Enugu, Imo, Delta, Oyo, Kebbi da Cross River.

” Binciken da muka gudanar a tsakanin karshen watan Fabrairu zuwa Maris ya nuna cewa an samu karin mutane 39 da suka kamu da cutar a wasu jihohi shida. Ba a samu wani ma’aikacin kiwon lafiya da ya kamu ba.

” Idan ba a manta ba tun da cutar ta bullo a wannan shekarar ma’aikatan kiwon lafiya 15 ne suka kamu da wannan cuta.

Ihekweazu yace a yanzu haka asibitocin dake kula da mutanen da suka kamu da cutar dake kasar nan na kula da mutane 69 da ake zaton sun yi mu’amula da mutanen da suka kamu da cutar.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa ta bada dala 400,000 da ma’aikatan ta domin ganin an an kawo karshen yaduwar wanna cuta a Najeriya.

Ihekweazu yace NFELTP, ma’aikatar aiyukkan gona da ma’aikatar muhalli sun amince su hada hannu da NCDC domin ganin an kawar da wannan cuta a kasar nan.

Hanyoyin guje wa kamuwa da zazzabin lasa sun hada da:

1. Da zaran mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.

2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.

3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci nesa da fitsari da kuma kashin beraye.

5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi.

Share.

game da Author