Zazzabin dake kama dawakai ya bullo a Kaduna

0

Likitocin dabobbi a jihar Kaduna sun bayyaa cewa cutar zazzabin dake kama dawakai da ake kira ‘Equine Influenza’ da turanci ya bullo a jihar.

Likitocin sun ga alamun haka ne a jikin wasu dawakai 18 a Zariya da Igabi inda hakan ya sa aka kebesu domin gujewa yaduwar cutar.

Alamun wannan cutar da za a gani a jikin doki sun hada da zazzabi, rashin iya cin abinci, ciwon gabobu, zuban majina, tari da sauran su.

Kwamishinan aiyukkan gona da dabobbi Manzo Daniel ya bayyana cewa gaggauta hana yaduwar wannan cutar ya zama dole ganin cewa Igabi da Zariya ne matattarar dawakai saboda anan ake akafi kiwon su saboda hawan sallah da kwallon dawakai.

Ya kuma ce gwamnatin jihar ta tanaji magunguna da allurar rigakafi domin hana yaduwar ciwon hakarkari dake kama dawakai, shanu da jakkai da ake kira ‘Contagious Bovine Pleuro Pneumonia (CBPP)’.

Daniel yace za a fara bada magungunan da allurar rigakafin a kananan hukumomin Kagarko, Kauru, Chikun, Giwa da Lere.

A karshe ya yi kira ga masu kiwon dabobbi da su ba gwamnati goyon baya da likitocin dabobbin domin kawar da cutar a jihar.

Share.

game da Author