Jam’iyyar PDP da ke adawa a jihar Jigawa, ta bayyana cewa mai yiwuwa ba za ta shiga zaben gwamnan jihar Jigawa ba da za a gudanar a ranar 9 Maris, 2019, idan ba a cire Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bala Senchi daga jihar ba.
PDP ta yi zargin cewa an tabka magudi a zaben shugaban kasa, an sayi kuri’u kuma ‘yan sanda sun rika cin zarafin magoya bayan PDP a jihar a zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya.
Dan takarar sanata, Mustapha Lamido ne ya bayyana haka a ranar Laraba da dare, cikin wata hira da aka yi da shi a Gidan Radiyon Freedom da ke Dutse, babban birnin jihar.
Mustapaha dan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ne.
APC mai mulki a jihar ce ta lashe zaben shugaban kasa, na majalisar dattawa da na tarayya kakaf a jihar jigawa.
Mustapha ya fito takarar sanatan Jigawa, amma wanda ke kai, Sabo Nakudu ya kayar da shi. sai dai kuma ya yi zargin cewa an tafka magudi da kuma cin zarafin ‘yan adawa a fadin jihar.
Ya koka sosai da jami’an tsaro wadanda ya ce sun nuna bangaranci a lokacin zaben.
Dangane da magudi kuwa, ya ce sau biyar ya na kiran kwamishinan ‘yan sanda ya na sanar da shi inda aka yi satar akwati, amma babu abin da aka yi.
“Ni dai ban ga abin da Kwamishinan ‘Yan sandan Jigawa ke yi a jihar ba, tunda dai an tashe shi daga jihar. Idan bai tashi daga jihar Jigawa ba, mai yiwuwa ne PDP ta kaurace wa zaben.” Inji matashin dan siyasar.