Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zangon sa na biyu zai tsaurara sosai a kan kudirori da ajandojin da ya yi wa ‘yan Najeriya alkawari.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi tawagar ministocin sa a Fadar Shugaban Kasa, a lokacin da suka je taya shi murnar cin zabe karo na biyu.
“Zango na na biyu, kuma wanda shi ne na karshe, ina jin zai yi tsauri sosai. Su jama’a akwai su da saurin mantauwa. Shi ya sa ma a lokacin kamfen na rika magana a kan abubuwan da ke gaban mu.” Inji Buhari.
Buhari ya kara da cewa dalili ma kenan ya ke ta yawaita tunatar da ‘yan Najeriya alkawurran sa kan magance tsaro, inganta tattalin arziki, samar da aikin yi da kuma dakile rashawa da cin hanci.
Baya ga ministocin kimanin su 20, akwai kuma Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, Shugaban Ma’aikata na Gwamnatin Tarayya, Winifred Oyo-Ita da kuma Mashawarcin Shugaban Ka a Fannin Tsaro, Babagana Monguno