Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya shirya komawa Daura ya zauna bayan ya kammala zangon sa na biyu cikin 2023.
Haka ya bayyana jiya Talata a wata ganawar sa da Sarakunan Gargajiyar kasar nan, a fadar sa a Abuja.
Sarakunan sun kai masa ziyarar murna lashe zabe ce a karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar da kuma Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi II.
Buhari ya yi kira ga sarakunan da su mara wa gwamnatin sa baya domin ya cimma dukkan kudirorin da ya sa a gaba a cikin wannan zango na sa biyu mai zuwa.
Wata sanarwar da kakakin sa Garba Shehu ya sa wa hannu, Buhari ya yi musu marhabin da ‘Next Level’, wani kirarin kamfen din sa a zaben 2019 da aka gudanar makonni biyu da suka gabata.
Buhari ya roke su da su taimaka wa gwamnatin sa wajen zakulo mabuyar duk wasu batagari da mabarnata da ke boye a cikin masarautun da ke yankunan su.
Buhari ya ce saka sarakunan gargajiya wajen zakulo mabarnata ya zama wajibi, saboda su na da masaniyar kowane lungu da sako na yankunan da su ke mulki.
“Kun san gidajen da duk ake boye wasu batagari kuma kun san gidajen da mutanen kirki da yaran kwarai suke.”
Daga nan sai Buhari ya ce babu wata gwamnati da za ta iya gudanar da abin a zo a gani ba tare da goyon bayan sarakunan gargajiya ba. Saboda haka ne ya ce ana matukar bukatar sa hannun su wajen taimaka wa gwamnati magance matsalar tsaro.
Daga nan sai ya shaida musu cewa a shirye ya ke bayan ya kammala zangon sa na biyu a cikin 2023 ya tattara kayan sa ya koma Daura da zama.
Yayin da Sultan na Sokoto ya mika sakon taya murnar daukacin sarakaunan ga Buhari, shi kuma Ooni na Ife kira ya yi ga Buhari ya zama shugaba na daukacin kasar nan da kuma al’ummar ta baki daya.