Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa zai kara wa mata da matasa gurabu a cikin gwamnatin da zai kafa ta zangon sa na biyu, na shekaru hudu masu shigowa daga ranar da aka rantsar da shi.
Buhari ya ce ya gamsu da rawar da mata da matasa suka taka wajen gwagwarmayar yakin neman sake zaben sa karo na biyu.
Dangane da wannan gagarimin korarin zaben sa zuwa ‘Next Level’ da suka yi ya ce shi ma ya yi alkawarin ba zai yi watsi da su a wannan sabon zangon sa na shekaru hudu da zai sake yi ba.
Ya bayar da wannan tabbaci ne jiya Lahadi a lokacin da ya ke jawabi a wurin walimar cin abincin dare tare da Reshen Mata da Matasa na Jam’iyyar APC.
An gudanar da dinar ce a Fadar Shugaban Kasa, domin murnar sake lashe zabe da Buhari da kuma jam’iyyar APC suka yi.
“Na yi farin cikin zuwan ku domin halartar wannan dina. Amma sai dai mu gode wa juna kenan a kan wannan nasara da mu ka sake samu. Tabbas mun gode wa Allah a kan wannan nasara da ya ba mu.” Inji Buhari.
Sai dai kuma ya ce sai fa mutane nagari, sahihai kuma masu nagarta zai dauka a cikin gwamnatin sa da zai kafa ta zango na biyu.
A wurin sai da Buhari ya sake nanata cewa a shekaru 16 da PDP ta yi a kan mulki, ba ta tsinana wa Najeriya komai ba.