Sanata Ahmed Lawan ya bayyana cewa idan aka zabe shi ya zama shugaban Majalisar Dattawa, zai yi jagorancin da babu nuna bambanci tsakanin ‘yan jam’iyya.
Lawan, wanda Sanata ne mai wakiltar Shiyyar Yobe ta Arewa, ya kuma yi alkawarin cewa zai bi dukkan abubuwan da jam’iyyar APC ta zartas.
Ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Abuja. Sanatan ya ce duk da cewa sanatoci sun fito ne daga jam’iyyu daban-daban, to akwai bukatar hadin kai a tsakanin su, domin cigar da kasar nan a gaba.
“Dukkan mu babu wanda ya zo don kishin kan sa, kuma babu wanda ya kawo kan sa. Kowa jama’a suka turo shi, kuma su suka zabe shi. Don haka gaba dayan mu ai kin jama’a da muke wakilta mu ke yi.
” Ba na jin a cikin mu akwai sanatan da za a kawo kudirin samar da tsaro ko wanda ya shafi ‘yan sanda ya ki amincewa da shi. Ko akwai? Ni na san babu.”
A kan haka ne sanatan ya ce sai an kauda bambancin jam’iyya sannan za a samu cimma hadin kai da cigaban kasa.
A karshe ya jaddada alwashin samar da jagoranci mai wanzar da daidai to da adalci a tsakanin mambobin Majalisar Dattawa, ba tare ta bambancin siyasa ba.