ZAMFARA: Mahara sun sace ’yan sandan mobal biyar, bayan sun bindige daya

0

Wasu mahara sun kai samame a wani ramin hakar ma’adinai sun bindige dan sandan mobal daya kuma suka yi garkuwa da sauran biyar masu gadi a wurin.

Wannan al’amari ya faru ne a Karamar Hukumar Anka, a ranar Laraba da ta gabata.

Dukkan ’yan sandan shida su na gadi ne a wurin hakar ma’adinan.

Wani da aka yi abin a kan idon sa, mai suna Salisu Lawali, ya shaida wa ’yan jarida cewa mahara sun kai samame kauyen Sunke, bayan sun bude wuta, sun kwace dukkan bindigogin da ke hannun ’yan sandan mobal shida, sannan a nan take suka bindige daya daga cikin su.

Ya ce maharan sun arce da ‘yan sandan su biyar, amma washegari suka sake su, ba tare da ba su bindigogin su ba.

Shugaban Karamar Hukumar Anka, Mustapaha Gado, ya shaida cewa an tura jami’an tsaron ne domin su rika gadin wurin hakar ma’adinan.

Ya tabbatar da afkuwar harin da kuma garkuwar da aka yi da jami’an mobal din su biyar.

Sai dai kuma ya ce an sake su bayan wasu sa’o’i da kama su.

“DPO na Karamar Hukumar Anka ya shaida min cewa an sako ‘yan sandan, amma kuma ba a maida musu bindigogin su ba.

“Tun can baya sai da muka rufe wurin, muka hana hakar ma’adinai, amma ana iya ganin wasu ‘yan kasashen waje jifa-jifa, saboda akwai yaran su a wurin..

“Bayan hukuma ta amince mana da hana hakar ma’adinai a wurin, masu aiki a wurin sai suka nemi jami’an tsaro da kan su domin su rika yi musu gadi.” Inji shi.

Share.

game da Author