ZABEN SHUGABAN KASA: Atiku ya gabatar da ainihin adadin yawan kuri’un da kowacce jiha ta samu

0

Tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya mika wa kotun sauraren korafin zaben shugaban kasa ainihin sakamakon zaben da kowacce jiha ta samu.

Atiku ya ce bisa ga sakamakon da na’urar tattara kuri’u na hukumar zabe, shine yayi nasa a zaben shugaban kasa ko tantama bayayi.

A bayanan da jam’iyyar PDP ta mika a gaban kotu ranar Laraba, sun nuna cewa na’urar tattara sakamakon zabe na hukumar INEC ya nuna jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben shugaban kasa da kuri’u miliyan 1.6.

Wannan daya ne daga cikin hujjoji 50 da jam’iyyar PDP ta mika a gaban kotun dake sauraron shari’ar zaben shugaban kasa da a Abuja.

Idan ba a manta ba tun bayan bayyana sakamakon zaben shugaban Kasa da hukumar zabe tayi jam’iyyar PDP ta yi watsi da wannan sakamako cewa jam’iyyar APC ta tafka magudi a zaben.

A sakamakon da aka bayyana bayan zaben, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben da kuri’u 15,191,847 inda Atiku ya samu kuri’u 11,262,978.

A bayanan korafin da PDP ta mika, ya nuna cewa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben da kuri’u 18,356,732 inda ya kada Buhari na Jam’iyyar APC da ke da kuri’u 16,741,430.

Bayan nan PDP ta ce takardan kammala jarabawar makarantan sakandare da Buhari ya mika ta boge ne domin a cewar su a lokacin babu jarabawar WASC, amma kuma ita Buhari yake gadara da.

Haka kuma lauyan Atiku da Jam’iyyar PDP ya mika wa kotu shaidar takardun watardun da aka shigar da sakamakon zabe, da wasu bayanai dake nuna yadda aka yi magudi da a wajen hada alkalumma sakamakon zaben da wasu bayanai.

Sai dai kuma a martani da jam’iyyar APC ta maida wa Atiku, jam’iyyar ta ce zautuwa ce Atiku yayi da jam’iyyar sa ta PDP fadin wai sune suka yi nasara a zaben shugaban kasa.

” Akan samu irin wannan rudewa da gigita dama idan aka yi wa mutum mummunar kayi irin wanda aka yi wa Atiku.

Ga takardun korafin da Atiku ya mika wa kotu

Share.

game da Author