ZABEN RIBAS: INEC ta watsa mana kasa a ido –Sojojin Najeriya

0

Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta bayyana cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta watsa mata kasa ido, kuma ta kwance mata zani a kasuwa.

Ta yi wannan bayani ne bayan da INEC ta zargi sojoji da ‘yan jagaliyar siyasa da laifin hargitsa zaben gwamna a jihar Ribas.

Hargitsin da ya faru ne ya tilasta INEC dakatar da ci gaba da tattara sakamako da bayyana sakamakon zaben.

Kakakin Rundunar Sojoji Bataliya ta 6 da ke Fatakwal, mai suna Aminu Iliyasu, ya ce sojoji sun yi nadama da jin haushin yadda INEC ba ta saka bayanan da sojoji suka gabatar wa Kwamitin Bincike na INEC da ta gabatar a Fatakwal a cikin binciken da ita INEC ta ce ta gudanar a Fatakwal ba.

“Wannan ya nuna rashin gaskatawar da INEC ta yi wa sojojin Najeriya, wadanda suka sadaukar da kan su matuka, domin ganin cewa INEC ta gudanar da aikin ta yadda ya dace.” Inji Iliyasu.

Daga nan kuma sai sojoji suka ce sun cika da mamakin ganin yadda INEC ba ta saka rahoton da aka kashe wasu sojoji biyu ta hanyar yi musu mummunan kisa.

Sun zargi daya daga cikin ‘yan sanda dogaran Gwamna Nysome Wike da ‘yan bindigar jagaliyar siyasa ne suka kashe sojojin a Karamar Hukumar Obio Akpor, a ranar 9 Ga Maris, 2019.

Sojoji dai sun ci gaba da bada misalai na irin kokarin da suka yi wajen ganin hargitsi bai barke a Jihar Ribas ba, kuma kamar yadda suka ce, sun yi iyakar kokari wajen tabbatar da cewa INEC ta gudanar da ayyukan ta na gudanar da zabe da tattara sakamako a jihar Ribas.

A kan haka sojojin sun fada da babbar murya cewa ba su amince da rahoton da kwamitin da INEC ta kafa ya fitar ba, wanda ya dora wa sojoji lafin hargitsa zabe.

Sannan kuma sun nuna damuwa da rundunar ‘yan sanda dangane da ba’asin da ta bayar da wanda ta ki bayarwa.

Share.

game da Author