Kotun dake sauraren karar sakamakon zaben Osun da jam’iyyar PDP ta shigar ta yi watsi da korafin jam’iyyar APC sannan ta tabbatar wa dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP Adeleke da kujerar gwamnan jihar.
Alkalai uku da suka yanke hukuncin wannan shari’a sun bayyana cewa zaben da aka maimaita a wasu mazabu bai bi tsarin doka ba.
A hukuncin alkalan sun ce karfa-karfa ne aka yi a zaben da aka maimaita wanda a dalilin haka ba zai zama dalili ko hujja ba na bayyana APC wanda ta yi nasara a zaben.
Kotun ta tabbatar wa PDP da wannan Kujera ta gwamnan Osun.