ZABEN KANO: Kotun Daukaka Kara ta share wa Abba Yusuf hanyar gwabza karo da Ganduje

0

A jiya ne Kotun Daukaka Kara ta wanke dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar PDP, Abba Yusuf, daga dakatarwar da BabbarKotun Tarayya ta yi wa takarar sa,

Kotun Daukaka Kara a karkashin shugabancin Mai Shari’a Daniel Kalio, ta amshi rokon da dan takarar ya yi tare da jingine hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yi wadda a baya ta ce ta haramta Abba da PDP su shiga takarar gwamnan jihar Kano, a bisa zarginn rashin yin zaben fidda-gwani.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Babbar Kotun Kano ta haramta takarar Abba Yusuf a bisa wata kara da daya daga cikin masu takarar gwamna a karkashin PDP tun a zaben fidda-gwani, Mohammed El-Amin ya kai cewa ba a yi zaben fitar da gwani ba.

A jiya Kotun Daukaka Kara ta hana INEC cire dan takarar PDP, Abba Yusuf daga cikin jerin ‘yan takarar gwamnan jihar Kano.

Da ya ke jawabi, Abba Yusuf ya ce shi dama bai damu ba, domin kawai matsala ce ta cikin jam’iyya, wadda wani hasalalle ya nemi ya yi amfani da ita domin ya dadada wa Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje rai.

Abba ya roki daukacin ‘yan PDP su fito kwan su da kwarkwata su jefa wa PDP da kuma shi kan sa kuri’a a ranar Asabar mai zuwa, domin PDP ta yi nasara a jihar Kano.

A yanzu dai Ganduje na fuskantar matsala a zaben da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa. Duk da cewa PDP ba ta samu kuri’u masu yawa a jihar Kano a zaben shugaban kasa ba, alamomi na nuni da cewa da dama daga cikin wadanda suka zafi Buhari, to a zaben gwamna, Abba na PDP za su zaba.

Wannan kuwa bai rasa nasaba da ibtila’in cusa miliyoyin daloli da aka fallasa Ganduje na yi, a cikin wasu faya-fayen bidiyo na soshoyal midiya da aka rika watsawa cikin 2019.

Da alama wannan kurwar ce ke ta bibiyar Ganduje har ranar zabe.

Share.

game da Author