Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa (INEC), ta tabbatar da cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zabukan da za a maimaita a yankunan da aka sanar cewa zabe bai kammalu a jihar Kano ba.
Kwamishinan Zabe na Jihar Kano, Riskuwa Arab-Shehu ne ya bayyana haka jiya Alhamis a Kano, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai.
Ya ce INEC ta turo Kwamishinonin Zabe daga Jihar Zamfara, Ogun da Kebbi domin su taimaka masa wajen karasa zaben da bai kammalu a jhar Kano ba.
Riskuwa ya ce za a sake zabukan ne a cikin wasu mazabu da rumfuna cikin Kananan Hukumomi 28 daga 44 da jihar Kano ke da su.
Ya ce gaba daya mutane 128,374 ne za su yi zaben a fadin rumfunan zabe 207 a ranar Asabar, 23 Ga Maris.
Ya ce an soke zaben gwamna a rumfuna 116 cikin kananan hukumomi 15, sakamakon hargitsin da ya afku makonni biyu da suka gabata a lokacin zaben gwamna.
Ya ce wannan soke zabe ya shafi kuri’u 73,173 da aka jefa a wuraren.
Sauran kananan hukumomi 23 kuma aringizon kuri’u ne aka yi har 55,151, a rumfunan zabe 92, ya sa tilas INEC ta soke zaben.
Ya ce tuni INEC a Kano ta karbi dukkan kayan aikin zabe kuma za ta raba su a yau Juma’a, domin gudanar da zaben gobe Asabar.