Gwamnatin Jihar Kano ta yi musanta rahotannin da suka ce an kashe mutane a lokacin zaben da aka maimaita a ranar 23 Ga Maris.
Gwamnatin ta kara da cewa ta na kalubalantar duk wanda ya san an kashe wani, to ya kawo hujja.
Haka Kwamishinan Yada Labarai, Mohammed Garba ya bayyana a taron manema labarai yau a Kano.
“Jam’iyyar PDP ta yi ikirarin cewa an kashe mutane biyu a Karamar Hukumar Nasarawa. Amma mun je yankin kuma mun je Karamar Hukumar Nasarawa, ba mu ga gawa ko hujjar cewa an kai musu rahoton kisa ba.
“To idan akwai wani mutum wanda aka yi kisa a gaban sa, ko kuma ma ina a Karamar Hukumar Nasarawa, ya fito ko ta fito ta bayyana.” Inji Garba.
Ya kuma ce ba gaskiya ba ne da aka ce an yi zarga-zanga a Kano, bayan bayyana sakamakon zabe.
Garba ya ce an yi ta watsa labarai marasa tushe da makama, kuma marasa sahihiyar hujja.
Ya ce gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma yaba da yadda ’yan jarida suka gudanar da aikin su a lokacin zaben.