ZABEN KANO: Ganduje ya fara manyan ayyuka a mazabun da za a sake Zabe a Kano gadan-gadan

0

Gwamnatin jihar Kano ta fara wasu manyan ayyuka
a karamar hukumar Nasarawa dake jihar domin karkato da ra’ayin mutanen yankin su zabi jam’iyyar APC a zaben da za a yi a mako mai zuwa.

Idan ba a manta ba zaben jihar Kano da wasu jihohi 5 bai kammalu ba a dalilin samun yawan kuri’un da aka soke sun fi adadin yawan ratar da jam’iyyar da ta yi nasara ta samu.

Hukumar zabe ta bayyana ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da za a yi zabe a wadannan wurare da aka soke a duk wadannan jihohi.

A jihar Kano, karamar hukumar Nasarawa ne tafi yawan kuri’un da aka soke Wanda a dalilin haka dukkan jam’iyyun da zasu fafata suke bin jama’a domin su zabe su.

Gwamnatin Kano cikin kwanaki uku kacal ta fara wasu manyan ayyuka a mazabar Gama dake karamar hukumar Nasarawa.

A cikin kwanaki uku kacal har gwamnatin Ganduje ta shimfida wa wannan gari lafiyayyar titi, sannan Kuma ta kwashe wani tarin bola da mazauna wannan unguwa ke fama da duk da toshe kunnuwar ta da gwamnati ta yi ada, sai gashi cikin kwana daya ana ta aiki babu kakkautawa.

Baya ga Titi da tarin bolan da ake kwashewa, ana Gina wa mutanen yanki rijiyoyin burtsate har guda 11.

Mutane da dama sun soki wannan aiki na gwamnati cewa tunda ba tayi ba sai ya zu da take neman kuri’un mutane.

Wani mazaunin garin Auwalu Danburawa, ya bayyana cewa aikin hanya ce aka fara da safe amma zuwa yamma har an kusa gamawa. Abin kamar almara. Yace unguwannin na fama da rashin ruwa, amma wannan rijiyoyi da ake haka wa zai sauwake wa mutane wahalar da suke fama da shi na wahalar ruwa.

Sai dai Kuma jam’iyyar PDP a jihar ta bayyana cewa wannan shine ainihin cin hanci da siyan kuri’u. Jam’iyyar ta ce sai da ake bukatar kuri’un jama’a sannan za a fara yi musu irin wadannan ayyuka.

Wani lauya Abba Hakima, ya bayyana cewa duk da cewa aiki ne ake yi don amfanin mutane, irin wannan aiki na riya ce.

” Mutanen da ake yi wa wannan sun dade suna bibiyan gwamnati, amma aka yi watsi da su sai yanzu da ake bukatar su shine za a fara yi musu aiki gadan gadan.”

Sai dai kuma gwamnatin jihar ta kare kanta inda ta ce aiki take yi wa mutane. Idan hakan zai sa ta jawo hankalin su su zabe ta, ita ba ta ga laifin yin ba.

Tun bayan bayyana sakamakon zaben jihar Kano da aka yi, garin Kano ta dau zafi inda magoya bayan Abba Yusuf na jam’iyyar PDP da na jam’iyyar APC suka ja daga.

Za a kammala zaben ne ranar 23 ga watan Maris.

Share.

game da Author