Mutanen unguwar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa jihar Kano kakar su ta yanke saka domin kuwa gwamna Abdullahi Ganduje ya bude wuta sai murza musu ayyuka yake yi babu kakkautawa.
Kafin a bayyana zaben gwamna da aka gudanar a fadin kasar nan ranar 9 ga watan Maris unguwar Gama ta na fama da matsaloli da dama sannan kuma gwamnati mai ci bata waiwaye su ba domin share musu hawaye.
Sai gashi da Allah ya kawo rabu wato gasassa daga sama cikin mako daya kacal sai zuba musu aiki ake yi kamar babu gobe. A cikin mako guda an markada musu sabbin tituna, an gina musu rijiyoyin burtsatse har 11 sannan ana ta ayuukan ci gaba a wannan mazaba.
A ranar Laraba kuwa mata ake ba jakukkunan haihu sannan wasu ana raba musu kudi har naira 10,000 ga kowacce.
Sai dai kuma bayan haka kungiyoyi da dama suna ta yin tir da wannan salo na Kamfen da siyan kuri’u da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya ke yi a wanann Unguwa.
Idan ba a manta ba Dan takarar gwamnan jihar Kano, na jam’iyyar PDP Abba Yusuf, ya kada gwamna Ganduje a sakamakon zaben da aka bayyana bayan kammala zaben. Sakamakon zaben ya nuna cewa kuri’un da aka lalata sun fi yawan ratar da Abba ya ba Ganduje.
A dalilin haka ya sa za a gudanar da zabe a wadannan mazabu da aka soke ranar Asabar 23 ga wata.

