ZABEN KANO BAI KAMMALU BA: Za a tafi zagaye ta biyu

0

Jihar Kano ma ta bi sahun jihohin da sai an tafi zagaye ta biyu kafin a iya tantance Wanda ya yi nasara a Zaben gwamnan jihohin.

Malamin zaben gwamnan Jihar da ya bayyana sakamakon Zaben ya bayyana cewa kuri’un da suka lalace sun fi yawan kuri’un ratar da wanda yayi nasara ya samu.

A Sakamakon da aka bayyana, Dan takaran gwamna na Jam’iyyar PDP Abba Yusuf ne ya lashe Zaben da kuri’u 1,014,474, shi ko gwamna mai ci Abdullahi Ganduje ya samu kuri’u 987,819.

Kuri’u 26,655 Abba yafi Ganduje da su.
Sannan kuma an lalata kuri’u 141,694 Wanda a dalilin haka yasa dole sai anyi Zabe a kananan hukumomi 22 da aka samu matsala da kuri’un su.

Share.

game da Author