Wakilin mu ya ci karo da dandazon jagororin Jam’iyyar APC da magoya bayan su suna siyan Kuri’u a boye. Wani da ya tattauna da wakilin mu ya ce duk wadanda suke da katin zabe na dindindin ne ake biya wadannan kudade domin siyan kuri’un su.
Ya kara da cewa ana biyan daga naira 3000 zuwa har 700.
An samu wadannan masu rabon kudi ne cikin daren Juma’a zuwa wayewar asabar din yau.
Wani da ya karbi tasa rabon ya shaida wa kilin mu cewa duk wanda yake da katin zabe na dindindin ne ake biya wannan kudi domin ya kada wa APC kuri’a.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=BYJLBcAcpMs&w=560&h=315]
Discussion about this post