Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa ya zama tilas a yi amfani da Na’urar Tantance Katin Zabe, da a Turance aka fi sani da card reader a zaben gwamna mai zuwa a ranar Asabar.
Kwamishinan Zabe Kuma Shugaban Kwamtin Wayar da Kai na INEC, Festus Okoye ne ya furta haka jiya Talata a Abuja.
Okoye ya ci gaba da cewa karya ce, kuma rudu kawai ake watsawa cewa INEC ta tunanin wancakalar da yin amfani da c’ard reader’ a zaben gwamnoni da na majalisar dokoki ta jihar a ranar Asabar mai zuwa.
“Ina tabbatar muku da cewa wannan rudu ne kawai da karairayi wasu ke yadawa cewa wai akwai yiwuwar a tilasta INEC yin watsi da na’urar tantance katin zabe, wato card reader.” Inji Okoye.
“Baya ga cewa tilas sai an yi amfani da ‘card reader’ a zaben, duk wanda ya nemi yin zabe ba tare da card reader ba, akwai dokar zabe da ta tanadi hukuncin dauri a kan sa.”
Ya ce ko a zaben shugaban kasa da da majalisar dattawa da ta tarayya, akwai wuraren da da yawa aka yi watsi da kuri’un da aka jefe, saboda ba a yi amfani da na’urar card reader ba.
Okoye yace bai ga yadda za a cewa wai za a janye amfani da card reader ba, musamman tunda kowa ya shaida cewa amfani da shi ya yi matukar rage harambe da daka-daka a lokacin zabe. Kuma kowa ya shaida haka.
Ya ce kowa sai ya yi amfani da ‘card reader’ an tantance shi kafin ya yi zabe, kuma babban laifi ne a kama mutum bai bai yi amfani da card reader ba, ko kuma yunkurin yin zaben ba tare da card reader ba
Don haka ya ce dukkan masu ruwa da tsaki a harkar zabe ya kamata su kara kwana da shirin sanin cewa sai da card reader ta tantance mutum sannan zai iya yin zaben.
A wata sabuwa kuma, Okoye ya jaddada cewa a wannan karon kusan a lokaci daya za a fara zabe a fadin kasar nan a ranar Asabar mai zuwa.
Ya ci gaba da cewa kuwa na’urar card reader za ta wadaci kowace mazaba, kowace rumba da kowane akwatin zabe.
Okoye yace INEC na nan ta na gagarimin shirin ganin cewa an fara jefa kuri’ar zaben gwamna da na majalisar dattawa da 7:30 daidai a dukkan fadin kasar nan.
Ya yi kira ga ma’aikatan INEC na wucin gadi da kada su bada kai borin masu yi musu wata barazana a yah au kan su.
Ya sha musu alwashin cewa za a kara matakan tsaron kare lafiya da rayukan kowa.
Discussion about this post