Jam’iyyar PDP ce ta yi nasara a Zaben gwamna da aka yi a Jihar Bauchi inda ta kada APC da gwamna mai ci Abubakar Mohammed.
A Sakamakon zaben da malamin Zaben gwamna na Jihar Bauchi ya bayyana a garin Bauchi, Sanata Bala Mohammed, Kauran Bauchi na Jam’iyyar PDP ne ya lashe Zaben da kuri’u 469,512, Inda gwamna mai ci na Jam’iyyar APC ya samu kuri’u 465,453.
Sai dai Kuma Kash, murna ta Koma ciki domin kuwa Hukumar Zabe ta bayyana cewa wannan Zabe bai Kammala ba domin kuwa ba a bayyana sakamakon Zaben karamar Hukumar Tafawa Balewa ba.
Sannan Kuma bisa ga sakamakon Zaben PDP ta na gaba da APC da ratar kuri’u 4059 inda aka samu lalatattun kuri’u ko kuma kuri’un da aka soke har 45,312. A Dalilin haka dole sai an sake Zabe a wuraren da aka soke zabukan su. Sannan Kuma za a sake Zabe a wuraren da aka suke Zabe a karamar Hukumar Tafawa Balewa.