ZABEN BAUCHI: Gwamna Abubakar ya kai karan Hukumar Zabe wajen Buhari

0

Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya kai karar hukumar Zabe wajen shugaban Kasa Muhammadu Buhari ranar Litini.

Koda ya ke gwamnan yace ya garzaya fadar shugaban kasa ne domin ya fede masa biri daga kai har bindi, domin yasan halin da jihar Bauchi take ciki game da zaben gwamna da aka yi da kuma irin hanyar da humar zabe ta dauka.

Idan ba a manta ba Hukumar Zabe ta amince da a sake kirgi sakamakon zaben da aka yi na karamar hukumar Tafawa Balewa sannan an tabbatar da yin aringizon kuri’un da aka soke a karamar hukumar Ningi cewa 2,533 ba 25,330 kamar yadda aka bayyana a da.

Gwamnan Bauchi ya ce wannan sake lale da hukumar zabe za ta yi ya saba ya dokar kasa domin doka ta ce muddun aka sanar da sakamakon zabe tabbas babu dalilin sake dawo da maganan baya kuma.

A hira da yayi da wakilin mu a fadar shugaban kasa Gwamna Abubakar ya ce ya garzayo domin ya sanar da shugaba Buhari halin da ake ciki ne a jihar.

” Na garzaya fadar shugaban Kasa ne domin in bayyana wa shugaba Buhari yadda zaben Bauchi ya kaya. Sannan kuma da yadda muka ji kwatsam cewa wai hukumar Zabe za ta sake kirga kuri’un da aka soke a karamar hukumar Tafawa Balewa, da kuma wasu matakai da aka dauka.

” Abin da hukumar Zabe ta yi saba wa doka ne domin ta riga ta bayyana sakamakon zabe da kuma wuraren da zabe bai kammalu ba, ta yaya kwatsam za a wayi gari ace wai kuma an jingine wancan hukunci, za a sake kirga zabe. Hakan bai yi ba.

Da aka tambaye shi ko ganawar sa da mataimakin shugaban kasa bai gamsu bane ya sa sai da ya ga shugaban kasa, gwamna Abubakar ya ce ya taho fadar shugaban kasa ne domin ya bashi cikakken bayani game da abubuwan da ke faruwa.

” Jihar Bauchi na nan lafiya kalau babu wani tashin hankali. Kuma ina so kowa ya sani cewa ba tsoron zaben Tafawa Balewa muke yi ba. Idan an so ma ko yau a buga, a shirye muke, kuma za mu yi nasara.

Share.

game da Author