Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar ya bayyana cewa zai yi amfani da duk wata dama da dokar kasa ta ba shi domin ya maka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kara a kotu.
Abubakar ya ce bai yarda da hukuncin da INEC ta yanke daga cewa za ta sake tattaro sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa har ta yi amfani da kididdigar da ta yi wa gyara ba.
Gwamnan ya na ja-in-ja da INEC ne a zaben gwamna da aka gudanar na ranar 9 Ga Maris, wanda aka samu tankiya a sakamakon zaben Tafawa Balewa.
Bayan an kammala hada sakamakon kowace karamar hukuma, Babban Jami’in Zabe na INEC na Jihar Bauchi, Farfesa Mohammed Kyari ya bayyana cewa zaben bai kammalu ba.
Sai dai kuma Kakakin Yada Labarai na INEC, Festus Okoye, ya ce INEC ta tura kwamitin bincike a Jihar Bauchi, wanda ya tantance inda aka yi aringizon kuri’un da a farko aka ce an soke kuma ya ji ba’asin ainihin abin da ya faru da sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa.
Bayan da kwamiti ya je, INEC ta ce za a ci gaba da tattara sakamakon, saboda akwai kwafen takardar sakamakon, wadda kowa ya shaida cewa ita ba ta salwanta ba.
A gobe ne Talata ne INEC ta ce za a ci gaba da tattara sakamakon.
Sai dai kuma Abubakar wanda dan takarar PDP, Sanata Bala Mohammed ya shiga gaban sa da yawan kuri’u, ya garzaya Fadar Shugaban Kasa da niyyar sanar da Shugaba Muhammadu Buhari abin da ya wakana a jihar sa, dangane da zaben gwamna.
A hirar da ya yi da manema labarai bayan ganawar sa a Fadar Shugaban Kasa, Abubakar ya shaida musu cewa.
Ya ce ya shaida wa shugaban kasa Baban Jami’in Zaben Jihar Bauchi da farko ya yi watsi da sakamakon Karamar Hukumar Tafawa Balewa, da kuma wasu rumfuna har 36 a fadin cikin wasu kananan hukumomi 15.
Gwamna Abubakar ya ce INEC ba ta da ikon warware hukunci ko abin da Babban Jami’in Zabe na Jiha ya rigaya ya bayyana.
Don haka ya ce abin da INEC ta yi haramtacce ne a dokar zabe na Najeriya.
Ya kara da cewa shi ba karar INEC ya kai wurin Buhari ba, domin INEC hukuma ce mai zaman kanta, kuma Buhari ba ya tsoma mata baki.