ZABEN 2019: Amurka ta ce an yi cinikin dimbin kuri’u kuma an razana masu zabe

0

Gwamnatin Amurka ta ce ko kadan ba ta ji dadin yadda zaben 2019 ya gurbace da abubuwan da ba daidai ba.

Gwamnatin ta Amurka ta ce daga rahotannin da ta samu daga masu sa-ido a zabe, an samu yawaitar tsorata masu jefa kuri’a, an ci kasuwar cinikin kuri’u, jami’an tsaro sun yi wa harkar zabe shiga-sharo-ba-shanu, sannan kuma a wurare da yawa hargitsi da tashe-tashen hankula sun rikita tsarinn zaben a sassa da yawa cikin Najeriya.

Haka Amurka ta bayyyana a cikinn wani rubutaccen sakon jawabi da ta aiko wa PREMIUM TIMES ranar Alhamis.

Sannan kuma ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a cikin zabe da kuma jami’an tsaro da su tabbatar da an gudanar da zabe cikin lumana, a yi adalci, kada a yi magudi ko murdiyya a zabukan da za a yi ranar Asabar a yankunan da INEC ta ce zabe bai kammalu ba.

Daga nan kuma Amurka ta mika sakon ta’aziyyar ta ga iyalan wadanda rikicin zaben 2019 ya yi sanadin rasa rayukan su.

Amurka ta kara jaddada cewa ita fa ba ta da wani dan takara da take goya wa baya, amma dai za ta ci gaba da bayar da goyon bayan da ta ke yi wajen ganin ingantacciyar dimokradiyya ta ginu, kuma ta tsaya da kafafun ta a Najeriya.

Share.

game da Author