ZABE: Sarkin Kano ya roki Kanawa su zauna lafiya

0

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga daukacin al’ummar Kano da su guji duk wani abin da zai iya haifar da hargitsi da tashe-tashen hankula.

Sanusi ya yi wannan kira ne biyo bayan sanarwar da INEC ta yi cewa zaben gwamna a jihar Kano bai kammalu ba.

Ya yi wannan kira ne yau Talata a lokacin da ya ke wa manema labarai jawabi a fadar sa.

Ya ce yin kiran ya zama wajibi, domin a yayyafa wa hayakin da ke neman tirnike jihar, ganin irin zaman fargaba, dardar da kuma yadda zukatan wasu da dama suka harzuka dangane da abin da ya biyo bayan zaben.

Sanusi ya ce tunda doka ce ta dora wa INEC karfin ikon bayyana sakamakon zabe, “to jama’a su daure su bi umarnin doka kuma su girmama dokar kasa.”

Ya ce INEC ke da ikon fadin sakamako, kuma tunda ta ce zabe bai kammalu ba, to a bi doka da umarnin INEC kuma a daure a kauce wa duk wani abin da ka iya haifar da fitintinu.

Daga nan kuma ya hori ‘yan siyasa da kada su rika yin furucin da zai kara tafarfasa siyasar Kano, kada yin hakan ya haifar da rikici.

“Kada ‘yan siyasa su maida cin zabe a matsayin wani abu na ko-a-ci-ko-a-mutu. Zabe gasa ce tsakanin bangarori biyu, tilas wani ya yi nasara, wani kuma ya dauki rashin nasara.”

Ya yaba da kokarin da jami’an tsaro suka yi, musamman ya ce irin kokarin da Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Wakili ya yi a lokacin zabe da kuma yadda ya yi kokarin kwantar da hankulan jama’a bayan kammala zabe.

Share.

game da Author